Ashe Wannan ne abinda ya faru da naziru sarkin Waka lokacin daya rubuta wakar Dawo Dawo ta labarina

Naziru sarkin waka ya kasance mawakine Wanda yafito daga arewacin najeriya daga Jahar Kano inda ya shahara wajan wakoki dasuka shafi na siyasa dana sarauta.

Acikin wata Hira da gidan jaridar BBC Hausa sukayi da shahararren mawakin ya bayyana irin kalubalen daya samu wajan kirkiro wakar labarina maisuna “Dawo Dawo” Wanda suka rerata shida sumayya.

Cikin hirar da akayi da mawakin ya bayyana irin wahalar daya shiga inda akwai lokacin da akagama wakar amman barayi sukazo Suka dauke computer da akayi wakar da ita kamar yadda zakuji daga bakinsa.

Ga video

Naziru ya bayyana cewar wannan wakar ta “Dawo Dawo” Shi Kansa baitaba samun kalu bale wajan rubuta Waka kamar yadda yasamu a wannan wakar ba Kuma cikin ikon Allah wakar ta karbu awajan mutane.

Kafin rubuta wakar Mun zauna nida Dan uwana Aminu Saira daraktan Shirin labarina munyi shawara dashi Akan munason mufito dawani Abu acikin wakar Wanda zaiyiwa mutane amfani matuka.

Shiyasa indai mutum yazauna ya saurari wakar “Dawo Dawo” tundaga farkonta har karshenta zaogane irin yadda wakar take wa’azantar da mutane gameda yadda Rayuwa take.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button