Dalilin Dayasa Baba Dan Audu Take Rashin Mutunci Acikin Shirin Labarina zango na 4

Dukwani makallacin shirin labarina yaga irin rashin mutuncin da baba Dan Audu ya aikata tundaga farkon season 4 har izuwa lokacin mutuwar Mahmud, inda abubuwan daya aikata lokacin mutuwar Mahmud sun matukar batawa ran makallata Shirin duk da Shirin ba gaskiya bane film ne.

Baba Dan Audu ya Fadi Dalilan Dayasa yake zafga rashin Mutunci Acikin Shirin Labarina. Inda ya Fara dacewar mutane basusan halin da baba Dan Audu yake ciki ba na kuncin Rayuwa da Talauci daya damesa.

Baba Dan Audu ya Kara dacewar inda wallahi inda wanine yake cikin halin dayake ciki zai iya aikata fashi da makami. Amman sabida Imani irinna baba Dan Audu baya fashi da makami Kuma Bai dauki Kayan Kowa ba kamar yadda zakuji acikin hirar da gidan jaridar BBC Hausa sukayi dashi a wannan bidiyon.

Ga video

Baba Dan Audu ya bayyana cewar bakowani mutum bane zaishiga irin halin da baba Dan Audu yake ciki ba ya jure Dole za’a samesa da Dan zamba cikin aminci, Dan cuwa cuwa Haka dai.

Cikin hirar baba Dan Audu ya bayyana cewar shiyanzu kokari yake yasamu ya tattata abinda zai samu ya hada yabar kasar domin ya koma saudiyya inda yafito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button