Innalillahi rashin lafiyar sani Garba Sk Ali Nuhu,Hadiza Gabon,Aisha Tsamiya da Abdulamart sun bada N950,000 akai sani Garba Sk asibiti

Kamar yadda muka kawo muku labarin rashin lafiyar daya daga cikin jaruman kannywood sani Garba Sk kan larurar ciwon sugar da ciwon Koda dayake damunsa.

Bayan bayyanar wani bidiyon sani Garba Sk Yana Karyata labarin mutuwarsa sani Garba Sk ya bayyana cewar kannywood sun taimakesa tun farkon rashin lafiyarsa harzuwa yanzu.

Sani Garba Sk yayi wannan tsokacine domin mutane masu zagin masana’antar kannywood sudaina Kan cewar masana’antar Basu taimaki jarumin dakomai ba.

Saidai rashin lafiyar jarumin rashin lafiyace Mai matukar cin kudi kamar yadda Fauziyya D Sulaiman Tafada domin ciwon nasa Dole sai ana tayashi da addu’a.

Ali Nuhu yabada tallafin naira dubu dari N100,000 inda Aisha Tsamiya tabada naira dubu dari itama N100,000 Hadiza Gabon itama tabada naira dubu dari biyu da hamsin N250,000 inda producer Abdulamart yabada tallafin naira dubu dari biyar N500,000 inda ayanzu Haka Jarumi sani Garba Sk Yana asibiti likitoci suna dubasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button