Innalillahi labarin mutuwar sani Garba sk ya girgiza kannywood domin sani Garba sk yananan da ransa

Innalillahi wa’inna ilaihi tabbas halin da jarumin kannywood sani Garba sk yake ciki abun tausayawa ne Amman jarumin Bai mutu ba kamar yadda mutane suketa wallafa labarin karya akan cewar jarumin ya mutu.

Saidai jarumin Yana cikin matsanancin ciwo inda yanzu Haka Yana kwance a asibiti Yana karbar kulawa daga wajan likitoci saidai cutar datake Damun jarumin shine cutar sugar da ciwon hanta Wanda wannan cututtuka guda biyu abun tsorone.

Kasancewar jarumin ya Dade Yana fama da Rashin lafiyar domin cutar takanzo Mai da zafi Bayan wasu lokuta saikuma sauki yazomai Amman ayanzu abun ya canja salo domin cutar tazowa jarumin da zafin gaske inda yake matukar Neman taimakon alumma daga fadin Duniya.

Masana’antar kannywood tabada gudunmawa akan rashin lafiyar sani Garba sk tun lokacin daya farata Haka zalika a halin yanzu damuke ciki akwai wasu Jarumi guda uku da producer Hausa dasuka taimakawa sani Garba sk da jumullar kudi kimanin naira dubu dari Tara da hamsin N950,000 domin akai jarumin zuwa asibiti.

Inda yanzu Haka jarumin Yana kwance a asibiti ana duba lafiyar tasa Amman haryanzu kofar taimako a bude take domin gamai bukatar taimako zai iya ziyartar shafin Instagram na Fauziyya D Sulaiman domin tuntubarsu akan halin da jarumin sani Garba sk yake ciki.

Kafin rashin lafiyar jarumin angansa awani sabon film maisuna “Gargada” na Kamfanin Ali Nuhu shirine Mai dogon zango inda sani Garba sk yafito a mijin Zahra Diamond.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button