Wasu jaruman kannywood sunbi tsarin Almajirai wajan rokon kudi

Wani abun ban mamaki daya faru acikin masana’antar kannywood shine yadda wasu daga cikin jaruman kannywood Sukabi sahun tsarin yadda Almajirai suke na rokon kudi awajan mutane.

Biyo bayan abinda yafaru da shahararren mawakin davido inda yafito ya bayyana cewar Yana Neman miliyan daya daga wajan abokanansa domin gudanar da shagalin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Inda cikin kwana daya abokanai da masoyan davido daga fadin Duniya Suka hadamai kudi kimanin naira miliyan dari biyu N200,000,000 Wanda wannan lamarin ya matukar girgiza mutane cikin awanni ashirin da hudu yasamu kudi naira miliyan dari biyu.

Ganin yadda mawaki davido yasamu wannan makudan kudaden yasa wasu daga cikin jaruman kannywood Suma Sukabi turbar dayabi wajan rokon masoyansu dasu taimaka su tura musu da kudi.

Inda jaruman dasukai wannan abun a kannywood sun hada da Garzali Miko, Lawan Ahmad, Auta waziri Dakuma Khadija yobe saidai bayan wallafa gajeran rubuta tareda saka lambar asusun bankinsu Akan cewar ataimaka musu da kudi hakan yasa mutane sunyi musu zagin cin mutunci.

Inda masoyan jaruman suke fadin Basu bane yakamata ace suna neman taimakon kudi daga wajan mutane akwai marasa lafiya a kwance a asibiti akwai Wanda suna bukatar taimakon abinci akwai Wanda suna bukatar muhallin dazasu zauna.

Domin wannan jarumai guda hudu dasuka fito suke rokon kudi awajan masoyansu Allah ya rufa musu asiri Amman suke kokarin karba Kudade awajan mutanen da Basu kaisu arziki ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button