Jarumar kannywood Maryam waziri (Laila Labarina) Tayi Auren Sirri Alhamdulillah

Fitacciyar jarumar kannywood Maryam waziri Wanda Kowa yafi saninta da Laila acikin shirin labarina na Kamfanin Saira Movies tayi auren sirri.

Munsamu cikakken rahoton labarin auren natane a shafin director shirin labarina Mai dogon zango Mal Aminu Saira Wanda shine shugaban Kamfanin Saira Movies.

Auren Maryam waziri (Laila Labarina) ya matukar bawa mutane mamaki domin bayan darakta Mal Aminu ya wallafa wani gajeran bidiyo Amarya Laila akwai Wanda Basu gasgata ba kasancewar acikin Shirin labarina ance ta tafi kasar waje cigaba da karatunta Haka zalika idan jarumai Mata ko maza a kannywood zasuyi aure sukan fito su sanarwa da Duniya cewar zasuyi aure.

Saidai haryanzu bamu samu cikakken rahoton wa jarumar ta aura ba Haka zalika a Ina aka daura Mata auren saidai wasu daga cikin jaruman kannywood sun matukar Taya Laila Labarina murnar Farin cikin auren datayi irinsu sarki Ali Nuhu da Teema Yola wato (Rukayya labarina).

Jaruma Maryam waziri tasamu daukaka sanadiyyar Shirin film din labarina Mai dogon zango na Kamfanin Saira Movies kasancewar irin rawar data taka acikin Shirin labarina yayi matukar birge mutane.

Saidai tun Bayan Shirin labarina zango na hudu da aka dauka ba’a sake ganin jarumar acikin wani sabon Shirin wasan Hausa ba, zamu iya cewar sabida jarumar Bata samu yadda daga wajan iyayenta ba.

Domin a wata Hira da aka tabayi da ita ta bayyana cewar Shirin labarina zango na daya Dana biyu data fito ba’a saniba agidansu sai bayan anfara haska Shirin ne Yan gidansu Sukaga fuskarta a akwatin talbijin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button