Da abani million 10 Gwanda abani Hadiza Gabon inji wannan saurayin

Wani labari Mai ban alajabi Kan wani Saurayi Wanda yayi ikirarin cewar da abasa kyautar Naira miliyan goma, gwanda abashi auren jarumar kannywood Hadiza Aliyu Gabon.

Wannan bashi bane Karo na farko da ake samun iri iren abubuwan alajabi da mutane suke fada akan jarumai Mata acikin masana’antar kannywood idan baku mantaba a makonni biyu dasuka wuce munkawo muku labarin yadda wani matashi ya kamu da soyayar Hadizan Saima jaruma Kuma uwa acikin masana’antar kannywood.

Saidai tun bayan bullowar wannan magana da saurayin yayi samari da Yan Mata suketa tafka muhawara a shafukan sada zumunta kasancewar a yanayin da ake ciki na karayar tattalin arziki da sauyin Abubuwa naira miliyan goma ba karamin kudi bace kamar yadda mutane suke bayyanawa.

Inda mafi rinjaye a shafukan sada zumunta sun soki maganar da saurayin tareda kiransa da sunaye iri daban daban, inda wasu suke ganin shirmene namiji yace da’a basa miliyan goma gwanda anbashi wata jaruma.

Inda wasu suke bayyana cewar yashiga rudin Soyayya ne domin Soyayya takan iya sa kowa ya aikata Abu akan abinda yakeso, Dan Haka basuga laifin wannan saurayin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button