Rawar da Fatima Ali Nuhu Tayi Ya Bayyana Wacece Fatima Ali Nuhu

Duk wani makallacin shirin Fina finan Hausa Yasan wacece Fatima Ali Nuhu kasancewar tana daya daga cikin jarumai masu karancin shekaru dasuka fara fitowa acikin Fina finan Hausa a shekarun baya dasuka wuce ita da kaninta Ahmad Ali Nuhu.

Fatima Ali Nuhu da kaninta Ahmad Ali Nuhu suna daya daga cikin kananan jarumai dasuka samu award duk da karancin shekarunsu acikin masana’antar kannywood.

Saidai Fatima Ali Nuhu daga Baya ta canja ra’ayi inda aka daina ganinta acikin Fina finan Hausa Wanda Babu Wanda Yasan dalilinta na barin harkar film saidai Fatima takan wallafa wasu hotunanta Dakuma gajerun bidiyon ta a shafinta na Instagram kamar yadda zaku gani.

Ga video

Saidai shima Ahmad Ali Nuhu ya daina fitowa acikin Fina finan Hausa domin cikin wata Hira da akayi dashi ya bayyana cewar Shi yanzu ya dakatar dayin film domin yafi son “football” ma’ana Kwallon kafa.

Wannan sune Dalilin Dayasa aka daina ganin Ahmad Ali Nuhu Dakuma Fatima Ali Nuhu acikin sababbin Fina finan Hausa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button