Abinda Maryam yahaya da Naziru Sarkin Waka Sukayi sun Bawa mutane mamaki

A yau labaran namu sunzo Kashi guda biyune ba kamar yadda muka Saba kawo muku Shiba inda gefe daya labarine akan Maryam yahaya dayan gefen Kuma labarine akan naziru sarkin Waka.

Idan baku mantaba munkawo muku labarai daban daban dangane da Halin Rashin lafiyar da jarumar kannywood Maryam yahaya take ciki Wanda a halin yanzu jarumar tasamu lafiya.

Saidai jaruma Maryam yahaya tanaci gaba da sakar wasu sababbin bidiyoyinta wanda masoyinta basajin dadin hakan kasancewar haryanzu Bata Gama samun Lafiya dari bisa dari ba Kuma abubuwan datakeyi acikin bidiyon abubuwane Wanda baikamata ace tanayi ba.

A gefe guda Kuma naziru sarkin Waka ya bayyana irin yadda yasha wahala wajan kirkiro wakar Shirin labarina maisuna “Dawo Dawo” kamar yadda zaku gani a wannan bidiyon.

Ga video

Naziru ya bayyana cewar wakar Dawo Dawo wata salon wakace Wanda idan ka zauna ka nutsu zakasan wakar tafita daban da sauran wakokin Hausa da aka sabayi domin cikin wakar akwai darasosin Rayuwa da mutum zai koya aciki.

Sannan kafin kammala wakar ansamu wani tsautsayi inda barayi Suka sace computer da akayi wakar Dawo Dawo Wanda hakan ya matukar janyo babbar matsala kafin naziru sarkin wakar ya sake rera sabuwar wakar tundaga farkon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button