Innalillahi Adam a zango Yana cikin Tashin hankalin da Bai taba Shiga irinsa ba

Biyo bayan rigimar data barke tsakanin Adam a zango da Ummi Rahab Wanda magana takici taki cinyewa.

An samu wasu bata gari sun sake yiwa Jarumi Adam a zango kutse cikin account dinsa na Instagram tareda sace mai account din, wannan kusan shine Karo na 6 da hakan take faruwa da jarumin.

A watannin baya kafin fara rikicin Adam a zango da Ummi Rahab, Adam a zango ya taba wallafa wani gajeran bidiyo a shafinsa na Instagram inda wani malamin addinin musulunci yake wa’azi akan musu aikata laifin Luwadi.

Inda a kasan bidiyon Adam a zango yayi Rubutu kamar Haka “Allah ubangiji ya Kare mu da aikata irin wannan laifin”

Saidai mutane sunyi tunanin jarumin ya wallafa wannan bidiyon ne domin Wanda suke aikata wannan abun su daina kokuma akwai Wanda yasani suna aikata irin wannan laifin yasa ya wallafa bidiyon domin sugani.

Bayan kwana biyu da wallafa bidiyon ansamu wasu sunyi kutse cikin Instagram account din jarumin tareda sace Masa account Dakuma lalata account, Wanda a karshe Adam a zango ya rasa account din nasa Mai followers miliyan daya dawani abu.

Tabbas mutane sunyita tofa albarkacin bakinsu inda suke cewa lallai Yan Luwadi ne suka sacewa Adam a zango account din domin bidiyon daya saka.

Baya ga Haka Adam a zango ya bude Instagram account kusan guda biyar duk ana sacesu, tabbas jarumin Yana cikin damuwa Akan abubuwan dasuke faruwa dashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button