Bani bace na Kashe Sani Garba Sk cewar jarumar kannywood Zainab Sambisa

Inbazaku mantaba munkawo muku rahotanni dasuka shafi lafiyar daya daga cikin jaruman kannywood wato Sani Garba Sk Wanda ansamu labarin mutuwarsa daga wani shafi a Facebook maisuna zainab Sambisa.

An wallafa cewar Allah yayiwa Jarumi sani Garba Sk rasuwa alhalin jarumin dai Yana kwance a asibiti bashida lafiya hakan ya biyo Bayan wani gajeran bidiyo da sani Garba Sk ya Fitar inda yake neman taimako daga wajan alumma akan rashin lafiyar datake damunsa.

Saidai jarumar kannywood Zainab Sambisa tafito ta nesa kanta daga wannan zargin da mutane suke Mata inda take cewar batada alaka da wannan shafin na Facebook Wanda ake amfani da sunanta domin ita Bata taba Bude shafin Facebook ba.

Dan Haka ba ita bace ta Fitar da sanarwar mutuwar sani Garba Sk batada masaniya akan wannan alamari daya faru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button