Duk Najeriya Babu Mai Gaskiya Da Tausayin Talaka Kamar Shugaban Kasa Muhammadu buhari Inji Dauda kahuta rarara

Shugaban mawakan jam iyar APC Alhaji Dauda kahuta rarara Kuma daya daga cikin masana’antar kannywood ya bayyana cewar duk Najeriya baiga Mai gaskiya Dama da shugaban Kasa muhammadu buhari ba.

Dauda kahuta rarara yayi wannan jawabin nasane yayin Hira da manema labarai acikin birnin Jahar Kano Dauda kahuta rarara Wanda ya kasance Dan asalin Jahar katsina saidai ayanzu Haka Yana zaune acikin garin Kano.

Sau dayawa ina duba wanda suke sauraran wakata ne idan zan rubuta bawai na kalli su da zan yiwa ba”

Kuma dalilin da yasa nafi yiwa Masari da Buhari wake shine, banga wanda ya kai Muhammadu Buhari Gaskiya ba a Nigeria kuma banga wanda ya kai Masari iya siyasa ba a jihar Katsina” acewar Dauda.

Daka karshe ya ce, maganar tsi-tsi da mutane suke tayi dama ai bazaka iya hana jariri kukaba indai bazaka bashi abinci ba, domin an kwashe shekara 16 ana barna a Nigeria, ga rashin kudin shiga, ga Korana duk idan aka kalla sun taimaka wajan tsintar kai a halin da ake ciki yanzu ba wai shugaban kasa bane.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button