Tabbas Babu Wanda Zai Iya Abinda Mawaki Ali Jita Yayi

Kamar yadda gidan jaridar BBC Hausa tasaba kawo wani shiri na musamman ga manya manyan jaruman kannywood Wanda suka hada damasuyun acting Dakuma masuyin wakoki.

A wannan Makon dai anyi babban bako mawakin Hausa maisuna Ali jita Wanda duk wani Mai sauraron wakokin Hausa shekara goma Sha biyar dasuka wuce Yasan wanene Ali jita kasancewar dadewarsa acikin masana’antar kannywood.

Ali jita an haifesa acikin garin Kano Amman ya girma a Lagos inda anan yayi primary da secondary daga baya Kuma ya dawo Jahar Kano inda yasamu damar cigaba da karatusa na gaba da secondary Wanda daga bisani Kuma ya tsunduma harkar wakoki.

Ali jita Yana daya daga cikin jerin mawakan Hausa Wanda tauraronsu haryanzu Yana haskawa a idon mutane kasancewar yadda ya canja salon wakokinsa suka koma na zamanin damuke ciki.

Ga video

Yanxu Haka mawaki Ali jita Yana zaune acikin garin Kano inda yanada Mata guda daya da Dakuma Yara biyar uku maza biyu mata.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button