Gaskiya tafito akan Kama Jarumi Ado Gwanja da Yan sanda sukayi

Fitaccen jarumin kannywood Kuma mawaki maifito acikin Shirin barkwanci ado Gwanja ya Karyata rade radin cewar ankamasa da aketa yadawa a kafofin sada zumunta.

Kamar yadda muka samu rahoto daga tashar Duniyar kannywood inda Suka Bayyana cewar sun tuntubi Jarumi Ado gwanja Kan gaskiyar lamari gameda zargin kamasa da akace anyi.

Inda suka bayyana cewar jarumin ya Karyata batun dayaketa yawo a kafofin sada zumunta nacewar hukumar tsaron Yan sandan najeriya ta kamasa.

Inda jarumin ya wallafa wani gajeran bidiyo a shafinsa na sada zumunta wato Instagram inda akaga Ado Gwanja awajan wani gagarumin biki da aka gayyaceshi a garin Kaduna.

Wannan lamarin ne yake Kara tabbatar da cewar Babu abinda yasamu mawaki ado Gwanja kamar yadda mutane suke yada labarin karya akansa.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button