Sadiq Sani Sadiq ya soki Gwamnati kan sabuwar cutar Omicron

Kasa da makonni biyu dai akaita yawaitar samun bullowar wata sabuwar nau’in cuta maisuna Omicron Wanda hakan yatashi hankalin masana kiwon lafiya na Duniya.

A inda jarumin kannywood Sadiq Sani Sadiq yayi martani maizafi kan wanna sabuwar cutar da ake ikirarin tashigo kasar Africa a halin yanzu damuke ciki ga abinda jarumin yake cewa.

“Ni narasa gane Kan irin wanga tsiya wai mutanennan sun dage dai sai sun wargaje Duniya musamman nahiyar africa. Shikenan babu gaira babu dalili anason Sai an kakabawa mutane talaucin Dole, munaji muna gani sunason sai komai yasake tsayawa cak. Mudai ayi hakuri abarmu muji da Abubuwan dasuka addabi arewa ma na rashin tsaro, duk da Haka Bai ishesu ba zasu Karo Mana wata masifar Azo ana garkame garuruwa Babu gaira babu dalili zasu Kara hargitsa tsohonnan Sudan cinye kudaden dabasu cinye ba anje anyi sabuwar rigakafi Dole saimun sake saye mu sake cin bashi. ALLAH KASANSU KASAN MUGUN KUDIRINSU ALLAH KAYI MANA MAGANINSU.

Wannan sune kalaman da Jarumi Sadiq Sani Sadiq yayi inda wasu daga cikin abokan sana’ar tasa suka tofa albarkacin bakinsu akan tsokacin da jarumin yayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button