Innalillahi Rayuwa Babu Tabbas mutuwar Mahmud (labarina)

Labarina Mai dogon zango wani shirine Wanda yakeda dumbin masoya sakamakon irin salon yadda labarin yazo yasha Bam Bam da sauran Fina finan Hausa.

Saidai mutuwar Mahmud acikin Shirin labarina yasa wasu daga cikin makallata Shirin sun nuna rashin jindadinsu kasancewar irin Shirin yadau zafi bayan Mahmud yasake dawowa cikin Rayuwar sumayya.

Saidai mutuwar Mahmud wasu daga cikin Shirin labarina sun dauka cewar Mahmud din ya mutu dagaske ne. Mahmud Yana Nan da ransa Bai mutu ba saidai acikin Shirin labarina ne yanayin yadda labarin yazo Dole Mahmud zai mutu.

A gefe guda Kuma haryanzu ana binciken inda za’a gano su wanene Suka sace Sumayya inda a wancan Makon akai tunanin cewar Baba Dan Audu shine ya sace sumayya. Inda bayan binciken da hukumar Yan sanda Suka gudanar alamu sun tabbatar da cewar baba Dan Audu bashida hannu acikin sace sumayya.

Saidai yayi amfani da sace sumayya da akayi wajan karbar kudin fansa awajan Yan uwan Sumayya inda daga karshe daya daga cikin Wanda sukai aika aikan karban kudin fansa ya tonawa baba Dan Audu Asiri awajan hukumar Yan sanda.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button