Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un Karima Izzar so

Sana’ar Fim Ta Canza Rayuwata Kuma Ina Kara godewa Allah da wannan ni’imar a gareni Khadijah Yobe

Fitacciyar jaruma a Shiri mai dogon zango na Izzar so Khadija Yobe, ta bayyana irin yadda harkar fim ta sauya Mata rayuwarta a dan karamin lokaci.

Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Dimukaradiyya a Kan sauyin rayuwar data samu in da take cewa.

“Gaskiya rayuwa ta cikin lokaci guda ta sauya tun da na fara fitowa a cikin shirin Izzar so, duk da cewar ba shi ba ne fim din dana fara yi, Amma dai shi ne ya fito da daraja ta mutane suka sanni sosai har na zama abar alfahari a cikin mutane, wannan yasa lokaci guda rayuwata sai ta sauya. “

Ta ci gaba da cewar” Sauyin rayuwar dana samu ya sa na san mutane Kuma an sanni yadda Hakan ya zamar da ni wata tauraruwar da a ke son gani a duk in da na je, don haka babu abin da zan ce wa Allah sai dai godiya, Kuma Ina fatan Allah ya Kara daukaka ni a cikin harkar na Kai in da ma ba na zaton zan kai, domin ko halin da na ke ciki ma a yanzu na samu kaina ne ba tare da na san zan Kai ba.

Jaruma Khadija yobe tanaci gaba da samun daukaka acikin masana’antar kannywood inda yanzu Haka tana fitowa acikin Fina finai daban daban sakamakon irin kokarin datake dashi wajan gudanar da ayyukanta.

Daga karshe ta yi roko ga Allah yasa ta gama harkar fim lafiya, yadda za a rinka tunawa da ita saboda gudummawar da ta bayar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button