Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un Rayuwa Babu Tabbas Allah sarki Sani Garba Sk

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un tabbas yakamata mutane mudinga hakuri Dakuma tawakalli a duk lokacin da muka tsinci kanmu cikin wani Hali.

Jarumin Shirya Fina finan Hausa sani Garba Sk Yana cikin mawuyacin Hali Wanda hartakai an kwantar dashi a asibiti sakamon yadda ciwon nasa yayi tsanani Wanda har hakan yasa jarumin yafito yayi bidiyo Yana Neman taimakon yan uwa musulmai dasu taimaka Masa.

Allah ya jarabci Jarumi sani Garba Sk da cutar ciwon sugar Dakuma cutar ciwon Koda Wanda hakan ya kwantar da jarumin kasancewar an bayyana cututtukan dasuke damun jarumin suna bukatar makudan kudade domin Nemo Masa lafiya.

Duk da irin taimakon dayake samu daga wasu daga cikin jaruman kannywood kamarsu Ali Nuhu, Hadiza Gabon, Aisha Tsamiya Dakuma producer Abdul Amart maikwashewa Wanda sun tallafamai da kudi kimanin naira dubu dari Tara da hamsin N950,000.

Saidai duk da Haka jarumin Yana bukatar taimakon alumar musulmai domin kudaden da ake nema Dan ceto lafiyarsa kamar yadda uwar Marayu Fauziyya D Sulaiman ta wallafa.

Sani Garba Sk Jarumi ne Wanda ya shafe sama da shekara ashirin acikin masana’antar kannywood Yana bada gudunmawa Kuma yafito acikin Fina finai daban daban.

Haka zalika Yana daya daga cikin jaruman dasuke fitowa acikin shirin “Gargada” Mai dogon zango na Kamfanin Ali Nuhu wanda ake nunasa duk ranar laraba da misalin karfe takwas na dare akan Manhajar YouTube a Tasha maisuna Ali Nuhu YouTube channel.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button