Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un Allah yayiwa Muneerat Abdulsalam rasuwa malamar lumancy

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un yanzu yanzu Muka samu labarin mutuwar Muneerat Abdulsalam Wanda akafi sani da malamar lumancy.

Muneerat Abdulsalam takasance malamar ma aurata kamar yadda wasu suke kiranta domin ta shahara wajan Saida maganin Mata daya shafi na ma aurata dadai sauransu.

Sanarwar mutuwar jarumar yafito daga shafinta na Facebook ne kamar yadda zaku gani acikin wannan hoton na Kasa.

Saidai haryanzu ba’asan wanene yayi amfani da shafin jarumar wajan bayyana rasuwar muneerat abdulsalam dinba.

Kafin mutuwar nata muneerat abdulsalam takasance babbar Yar kasuwace inda take kasuwancin abubuwan dasuka shafi magungunan dasuka shafi harkar ma’aurata Dakuma samari da Yan Mata.

Haka zalika a watannin baya dasuka wuce anga yadda jarumar tafito kafofin sada zumunta inda take kalubalentar mutane Kan yadda suke nuna Mata kiyayya domin tana harkar magungunan ma’aurata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button