Lawan Ahmad ya zagi mahaifiyar Sadiq Sani Sadiq akan rokon kudi dayayi awajan masoyansa

Biyo Bayan yadda mawakin kudancin najeriya davido yasha alwashin cewar Yana bukatar abokanansa da masoyansa dasu hadama kudi kimanin naira miliyan daya domin ya gudanar da shagalin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Hakan yasa cikin awanni ashirin da hudu mawaki davido yasamu kudi kimanin naira miliyan dari biyu wannan abun yatashi hankalin Duniya inda wasu daga cikin jaruman kannywood Sukibi irin wannan salon inda Lawan Ahmad yafito yayi bidiyo Yana rokon masoya Annabi dasu taimaka shima su turamai da kudi.

Saidai bayan fitowar bidiyon nasa Jarumi Sadik Sani Sadiq yafito yayi wani gajeran bidiyo duk da baikama suna ba acikin bidiyon nasa Amman alamu sun nuna Yana maganar tasane akan jaruman dasuka fito suna rokon kudi awajan masoyansu kamar yadda zaku gani acikin wannan bidiyon.

Ga video

Inda Lawan Ahmad yaji haushin abinda Jarumi Sadiq Sani Sadiq yayi inda takai harya zagi mahaifiyar Jarumi Sadiq Sani Sadiq inda shikuma Sadiq Sani Sadiq yake tambayar Lawan Ahmad shin meyayi yasa ya zagesa.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button