Naziru Sarkin Waka ya haddasa wata sabuwar rigima innalillahi wa’inna ilaihi raji’un

A jiyane shahararren mawakin Hausa naziru m Ahmad Wanda akafi sani da naziru sarkin Waka ya wallafa wani hoton feji daga shafukan Al-Qur’ani inda ya zagaye wasu kalmomi daga cikin Aya ya (34) acikin suratun nisa’i ayar na fadin (arrijalu kauwamuna alannisa’i) inda ya zagaye dai dai inda ake cewa (wadribuhunna) Wanda fassarar Kai Tsaye na nufin ku dakesu.

Saidai tun bayan wallafa wannan hoton wani shafi daga cikin Al-Qur’ani maganar ta zamto abun magana a kafofin sada zumunta inda wasu sukaita kushe abinda naziru sarkin wakar yayi tareda fadin maganganu marasa Dadi akansa.

Inda naziru sarkin wakar a kasan hoton ya rubuta cewar (To nidai Naga ayar datace ka daki matarka idan abun yaci tura….saidai a tayani duba wadda tace Kar adaki Mata nagode. Gadai cikakken hoton a Kasa domin Kuma kugani.

Saidai Nanda Nan mutane sukaita raddi akansa inda wasu suke fadin cewar ai shima ya’ya Mata yake haifowa Dan Haka Allah ya hadasu da mazajen dazasu dinga dukansu.

Haka zalika wannan magana ta naziru Sarkin Waka tadau matukar zafi Domin an Ware Mata waje a shafukan sada zumunta inda haryanzu ana tafka muhawara akan wannan batun na naziru sarkin Waka.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button