Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un Allah yaji kanki da Rahama ya gafarta Miki

Duk Kan ma Rai mamacine a yaune Muka samu rahoton rasuwar Yar daya daga cikin jarumai Mata iyaye a masana’antar kannywood wato Maryam CTV.

Allah yayiwa babbar yarinyar jaruma Maryam CTV rasuwa, labarin mutuwar yafito ne daga shafin sada zumunta na sarki Ali Nuhu kamar yadda shima yasamu labarin mutuwar ne daga shafin gwammaja entertainment.

Saidai wasu ansamu sabani inda wasu suke zaton cewar jarumar kannywood Maryam CTV itace ta Rasu inda ba Haka bane cikakken labarin domin kuwa babbar yarinyar jarumar ce Allah yayi Mata rasuwa Bawai jarumar ba.

Saidai wasu daga cikin makallata Shirin Fina finan Hausa sun shiga tunanin cewar Daman jaruma Maryam CTV tana yara Wanda ta haifa.

Tabbas jaruman kannywood Wanda suke fitowa a matsayin iyaye sunada manyan ya’ya Wanda Duniya Bata San dasu ba domin basuda alaka da fitowa acikin Fina finan Hausa shiyasa mutane basa ganin fuskokinsu.

Inbaku mantaba a watannin baya dasuka wuce anga jaruma Hafsat Idris ta aurar da babbar yarinyarta Wanda hakan ya matukar bawa mutane mamaki inda suke fadin Daman Hafsat Idris tanada babbar yarinyar datakai munzalin aure.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button