Kalli yadda Fati Washa ta maye gurbin Maryam waziri (Laila Labarina) acikin Shirin labarina

Tun bayan bayyanar hotunan auren jarumar Shirya Fina finan kannywood wato Maryam waziri Wanda akafi sani da (Laila) acikin Shirin labarina Mai dogon zango Wanda ke zuwa a tashar arewa24 duk Ranar juma’a da misalin karfe 9:00pm na dare.

Mutane sunyita tambayar shin wace jaruma ce Zata maye gurbin Laila acikin Shirin labarina kasancewar acikin Shirin farkon zango na hudu an nuna cewar Laila ta tafi kasar waje domin cigaba da karatunta.

Kwatsam Kuma saiga labarin Aurenta ya riske masoyanta dama abokanan sana’arta a masana’antar kannywood Wanda hakan yasa mutane Suka Fara tunanin wacece Zata maye gurbinta tareda jiran abinda darakta malam Aminu Saira zai fada akan Wanda Zata maye gurbin Nata.

Saidai a daren jiyane daraktan Shirin film din labarina Mal Aminu Saira ya wallafa wasu hotunan jaruma Fati Washa inda yake bayyana cewar (idan Fati Washa tafito acikin Shirin labarina wani matsayi kuke ganin Zata taka).

Tun a daren jiyan makallata Shirin labarina Suka Fara bayyana cewar alamu sun nuna cewar Jaruma Fati Washa itace Zata maye gurbin Maryam waziri (Laila) acikin Shirin labarina Mai dogon zango.

Kucigaba da bibiyar shafinmu domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button