Shagalin bikin auren Minal Ahmad da tsohon mijin Momee Gombe Ya Girgiza Kannywood

Wasu kyawawan hotunan jarumar Shirya Fina finan Hausa Minal Ahmad ya matukar daukar hankalin mutane inda aka wallafa hotunan a shafin Instagram na kannywood.

Cikin hotunan anga tsohon mijin Momee Gombe tareda jaruma Minal Ahmad wanda hakan yasa mutane sunfara tambayar kansu shine Daman Minal da tsohon mijin Momee Gombe suna Soyayya ne.

Hotunan dai sun bayyana yadda akeyin (pre wedding pictures) ma’ana hotunan da amare sukeyi kafin ranar daurin aurensu.

Saidai Koda shafin official kannywood suka wallafa wannan zafafan hotunan Basu bayyana cewar hotunan na daurin auren jarumar bane inda hakan yasa anbar mutane cikin wani yanayi na kullewarkai.

Bisa la’akari da yadda a kwanannan akai auren jarumai Mata guda biyu acikin masana’antar kannywood cikin sirri Wanda sai Bayan an daura aurenne sannan mutane suke sani wannan jarumai sune Laila tacikin shirin labarina Dakuma Rahama MK Matar Bawa maikada acikin Shirin Kwanacasa’in.

Kucigaba da bibiyar shafinmu domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button