Yanzu Mansurah isah Ta tonawa Sani Danja asiri akan Mutuwar aurensu

A KARO na farko, babbar furodusa a Kannywood, Mansurah Isah, ta yi bayani mai ɗan tsawo kuma kai-tsaye dangane da mutuwar auren ta da fitaccen jarumi kuma mawaƙi Sani Musa Danja, inda ta bayyana cewa ita kaɗai ta san wahalar da ta sha a zaman ta da shi.

Haka kuma ta ce rabuwar su ba ta sanya ta ɗauke shi a matsayin abokin gaba ba.

A wata hira da aka yi da ita a jaridar Daily Trust, Mansurah ta ce wahalar da ta sha, ko wani abokin gabar ta ko ‘ya’yan shi ba za ta yi fatan su sha irin ta ba.

A hirar, wadda mujallar Fim ta fassaro, tsohuwar jarumar ta ce mutane da ba su san halin da ta shiga a auren ta ba sun yi ta gaya mata baƙaƙen maganganu a lokacin da auren ya mutu.

Ta ce: “Mutane sun yi ta gaya mani magana a soshiyal midiya, da sauran kalamai na ɓatanci. Amma tuni na ci gaba da rayuwa ta.”

Kuma ta yi nuni da cewa, “Idan mace na shan wahala a gidan auren ta kuma ta yi shiru ba ta faɗa wa kowa ba, to idan ta mutu a ƙarshe sai mutane su ce me ya sa ba ta yi magana ba. Idan kuma ta buɗe baki ta yi magana ta nemi haƙƙin ta wanda har ya kai ga an sake ta, sai kuma mutane su koma su ɗora mata laifi. Hatta waɗanda ba su yi auren ba sai su riƙa gaya mata magana. Duk irin wannan ya faru a kai na.”

A kan batun ganin ta da aka yi da Sani a wajen fara haska fim ɗin ta mai suna ‘Fanan’ a gidan sinima kwanan baya a Kano, Mansurah ta faɗa wa jaridar cewa to ai tsohon mijin nata ba abokin gabar ta ba ne.

Ta ce, “Ni ban ga wani laifi a ciki ba. Shi ne uban ‘ya’ya na, kuma aboki na ne sannan abokin aiki. Saboda haka na kasa gane abin da ya sa mutane su ke wannan maganar. Mu na cikin rayuwar zamani ne yanzu; don mun rabu ba ya nufin mu na gaba ne.”

Da aka yi mata zancen yadda rayuwa ta kasance a gare ta tun bayan mutuwar auren, sai fitacciyar furodusar ta ce da man ta san za a yi mata wannan maganar, kuma ta daɗe ta na tunanin amsar da za ta bayar wadda ba za ta haifar da hayaniyar da za ta taɓa mutuncin ta da na iyalin ta ba.

Mansurah ta ce a taƙaice dai amsar ita ce ta na kira ga ‘yan matan da ba su riga su ka yi aure ba da ma zawarawa cewa su dinga yin haƙuri. “Allah ya san halin da su ke ciki, kuma ya fi kowa sanin abin da ya sa auren su ya mutu da kuma yanayin da su ka tsinci kan su a ciki,” inji ta.

A game da fitowa a fim da ‘ya’yan ta ke yi, Mansurah ta ce a fim ɗin ta ne kaɗai su ke fitowa, kuma su na yi ne ba don kuɗi ba.

Ta ce, “Har yanzu ƙananan yara ne, amma idan sun girma sun zaɓa wa kan su shiga harkar fim, to ba za mu samu matsala da wannan ba. Rayuwar su ce, illa iyaka dai mu nuna masu abin da ya dace su yi.” 

Mansurah da Sani sun yi aure ne a cikin 2007, kuma sun haifi ‘ya’ya huɗu – mace ɗaya (Khadijatul Iman) da maza uku (Khalifa Sani, Yakubu da Yusuf).

Labarin mutuwar auren su da ya ɓulla a ƙarshen watan Mayu 2021 ya girgiza jama’a matuƙa, musamman a soshiyal midiya inda ya janyo surutai masu yawan gaske.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button