Tsohuwar Matar Adam a zango ta farko tadawo harkar fina finan Hausa

Rahotanni sun bayyana cewar matar Jarumin Kannywood ta farko Adam A Zang, mai suna Amina Uba Hassan, ta dawo harkar fim gadan gadan.

Tsohuwar matar Jarumin wacce aka fi sani da Maman Haidar, ta fara shirin fim ne tun a shekarun 2000 kafin daga bisani kuma suka yi auren sunnah da Jarumi Adam A Zango a Shekarar 2007.

Babu wani cikakken dalili a hannu sai dai bayan sun haifi ɗan su na farko a shekarar 2008, sai kuma aka sami labarin ya sake ta bayan watanni biyar da haihuwar ta.

Bayan tsawon lokacin baa jin ɗuriyar ta ba sai dai yanzu Amina ta fara bayyana a sabon shirin kamfanin 2Effect mallakin jarumi Sani Danja, shirin mai dogon zango (Gidan Danja) wanda ake haskawa a tashar Arewa24 mako mako.

Amina ta bayyana cewar ta dawo tsohuwar harkarta gadan-gadan kuma babu gudu babu ja da baya, kuma tace tana alfahari da masoyan ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button