Dawowar Tsohuwar Matar Adam a zango harkar film ya janyo cece kuce acikin kannywood

Rahotanni sun bayyana cewar matar Jarumin Kannywood ta farko Adam A Zang, mai suna Amina Uba Hassan, ta dawo harkar fim gadan gadan.

Matar Jarumi Adam a zango Wanda suka rabu a shekarar 2008 bayan sun haifi yaro Wanda ake kiransa da suna Haidar, Haidar dai shine yaron Adam a zango na farko Wanda asalin sunansa shine Ali Adam a zango ya zabi yasakawa yaron nasa suna Ali sakamakon irin abokantakar dake tsakaninsa da Jarumi Ali Nuhu a shekarun baya.

Tsohuwar matar Jarumin wacce aka fi sani da Maman Haidar, ta fara shirin fim ne tun a shekarun 2000 kafin daga bisani kuma suka yi auren sunnah da Jarumi Adam A Zango a Shekarar 2007.

Tsohuwar Matar Jarumi Adam a zango bayan dawowarta masana’antar kannywood tafito awani film maisuna “Gidan Danja” na Kamfanin 2effect mallakin sani Musa Danja da Yakubu Muhammad.

Amina ta bayyana cewar ta dawo tsohuwar harkarta gadan-gadan kuma babu gudu babu ja da baya, kuma tace tana alfahari da masoyan ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button