Innalillahi wa’inna ilaihi Allah yayiwa Jarumi sani Garba Sk rasuwa yanzunnan Allah yaji Kansa da Rahama

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un Allah Mai yadda yaso yanzu Muka samu labarin rasuwar daya daga cikin jaruman kannywood sani Garba Sk.

Sani Garba Sk kafin rasuwarsa yakasance daya daga cikin jaruman kannywood Wanda suka shafe sama da shekara goma Sha biyar acikin kannywood, yafito acikin Fina finai daban daban.

Kafin rasuwar sani Garba Sk yayi fama da Rashin Lafiya na ciwon sugar Dakuma ciwon Koda inda a Makon daya wuce yafito Yana neman taimako awajan alummar musulmai akan cutar data damunsa domin za’ayi Mai aiki a asibiti.

Inda wasu daga cikin manyan jaruman kannywood suka fito Suka taimakawa da jarumin da kudi Wanda suka hada da Ali Nuhu ya bada N100,000 jaruma Hadiza Gabon tabada N250,000, Aisha Aliyu Tsamiya tabada N100,000 inda producer Abdulamart yabada N500,000 inda jumullar kudin suka Kama naira N950,000.

Muna rokon Allah ubangiji ya gafartawa Jarumi sani Garba Sk Allah ya haskaka kabarins yasa ya huta Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button