Tashin hankalin da jaruman kannywood Suka shiga sakamakon rasuwar sani Garba Sk

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un kullu nafsin za’ikatil maut dukkan Mai Rai mamacine a yammacin jiya laraba Sha biyar ga watan dizembar shekarar dubu biyu da ashirin da daya Allah ya karbi ran daya daga cikin jaruman kannywood sani Garba Sk.

Sani Garba Sk kafin rasuwarsa yasha fama da matsananciyar jinyae ciwon sugar da ciwon Koda Wanda ya shafe shekaru, inda a makonni biyu dasuka wuce anga yadda jarumin yasa akayimasa bidiyo Yana Neman taimakon kudi awajan mutane.

Rasuwar sani Garba Sk ta girgiza manyan jaruman kannywood irinsu Ali Nuhu, Adam a zango, Yakubu Muhammad, Aisha Humairah, Fati shuuma, Tijjani Asase, Ramadan booth, Amal Umar dadai sauransu.

Jaruman Kannywood mazansu da matansu sun nuna alhinin mutuwar daya daga cikin abokin sana’arsu Kuma amininsu inda sukaita wallafa hotunansu tareda yimasa addu’ar Allah ubangiji yaji Kansa da Rahama yasa Aljanna makomarsa.

Sani Garba Sk ya shafe sama da shekara goma Sha biyar Yana fitowa acikin Fina finan kannywood domin Yana daya daga cikin jaruman dasuka jajirce wajan cigaban masana’antar Shirya Fina finan Hausa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button