Kalli abinda ya faru awajan jana’izar Sani Garba Sk innalillahi wa’inna ilaihi raji’un

Rasuwar sani Garba Sk tana daya daga cikin rasuwar data girgiza kannywood kasancewar yadda sani Garba Sk yake dakuma matsayinsa acikin masana’antar kannywood.

Sani Garba Sk kafin rasuwarsa yasha fama da ciwon sugar Dakuma ciwon Koda Wanda jarumin yasha wahala matuka Haka zalika abokan sana’arsa acikin kannywood sun taimakesa lokacin rashin lafiyar tasa.

Inda a kwanannan kafin rasuwarsa yafito yayi bidiyo yana neman taimako inda jaruman kannywood Suka tallafamai fa kudi kimanin naira dubu dari Tara da hamsin. Ali Nuhu yabada N100,000 Aisha Tsamiya tabada N100,000 Hadiza Gabon tabada N250,000 saikuma producer Abdul Amart yabada N500,000

Sani Garba Sk yasamu shaida masu kyau daga wajan abokan sana’arsa a masana’antar kannywood Dakuma abokansa na kungiyar yabon fiyayyen halitta Annabi Muhammad s.a.w.

Bayan rasuwar sani Garba Sk Jarumi Tijjani Asase ya wallafa wani bidiyon Jarumi sani Garba Sk a shafinsa na Instagram inda akaga jarumin Yana qasidar yabon Annabi Muhammad s.a.w kamar yadda zaku gani acikin wannan bidiyon.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button