Sabuwar Salma Tashirin Kwanacasa’in tanashan zagi sakamakon wasu hotunan tsaraicinta dasuka bayyana

Duk Wani makallacin shirin Kwanacasa’in zaiga dawowar da akayi acikin Shirin Kwanacasa’in zango na 6 Wanda yake zuwa a tashar arewa24 duk Ranar lahadi da misalin karfe takwas na dare zaiga an bayyana wata sabuwar jaruma a matsayin Salma.

Acikin a ata Hira da akayi da daraktan Shirin Kwanacasa’in Salisu T balarabe ya bayyana cewar Dalilin Dayasa aka cire Salma babban daliline domin daga gidansu matsalar tazo Bawai daga tashar arewa24 bane.

Daraktan ya Kara da cewar kafin mufara daukar zango na 6 na tuntubi jarumar Akan cewar zamu Fara daukan zango na shida zata samu damar fitowa? Ta bayyana cewar bazata samu Dama gaskiya. Takara da cewar matsalar itama badaga wajanta bane daga mahaifantane.

Wannan Dalilin Yasa aka Fara Nemo jarumai dazata taka irin rawar da Salma take takawa da aka zauna aka tantance aka samo mawakiyar hip-hop princess mufeedah Wanda yanzu take fitowa a matsayin Salma.

Dama kafin tafara fitowa acikin Shirin Kwanacasa’in mawakiyar hip hop ce tana wakoki daban daban, saidai bayyanar wasu hotunanta a shafin sada zumunta yasa mutane sunyita sukar jarumar da maganganu marasa Dadi akan irin shigar banzar datakeyi.

Saidai har izuwa yanzu jarumar Bata fito tayi wani korafi kokuma nuna ranta ya baci dangane da zagin da mutane suke Mata ba.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button