Tashin hankalin da Momee Gombe Tashiga Bayan tsohon mijinta zai auri Nana izzar so

Wani sabon alamarin dake Shirin faruwa acikin masana’antar kannywood inda wasu hotunan tsohon mijin Momee Gombe Adam fasaha tareda Nana izzar so suke yawo a kafofin sada zumunta.

Tsohon Mijin maimunat Abubakar, Wanda akafi sani da Momee Gombe zai angwance da daya daga cikin jaruman kannywood Minal Ahmad Wanda aka sani da Nana acikin Shirin izzar so.

Tsohon Mijin Momee Gombe Adam fasaha dai cikakken Dan masana’antar kannywood ne, Wanda Kuma ya Dade sosai acikin masana’antar saidai bakowa bane yasansa kasancewar baicika fitowa acikin Fina finai ba.

Dama mutane suna fadin meyasa Yan kannywood Basu fiye auren junansu ba, ma’ana idan namiji a kannywood zaiyi aure saiya fita waje yaje ya Nemo Mata Haka zalika idan mace zatayi aure itama saita fita wajan masana’antar tanemo mijin aure. To Adam fasaha dai gashi zai sake angwancewa da jarumar kannywood akaro na biyu.

Tunidai hotunan Nana izzar so da agonta Adam fasaha sukaita zagaye shafukan sada zumunta inda mutane suketa musu fatan alkairi tareda addu’ar Allah ubangiji yabasu Zaman lafiya. Gadai wani cikakken videon hotunan shagalin bikin.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button