Kalli wasu Abubuwa da aka gano Bayan binne gawar marigayi Sani Garba Sk innalillahi

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un tabbas Rayuwa Haka take sai mutum baya Duniya ake ganin wasu alkairansa Wanda yayi da mutane Basu taba saninsa ba.

Mutuwar sani Garba Sk tasa yanzu angano wasu abubuwan da Marigayi sani Garba Sk yayi Wanda wasu daga cikin abokan sana’arsa a kannywood Basu taba sanin wannan abunba.

Akwai wani abun alkairin da marigayin yatabayi lokacin dasuka taba zuwa kasar Niger wasa dashi dasu Ali Nuhu da sauran jarumai kusan shekara goma Sha biyar dasuka wuce.

Bayan kammala wannan wasan da jaruman sukayi agidan Wasa saiya zamto cewar an hanasu hakkinsu wato kudin wasan dasukayi inda dukkan jaruman hankalinsu ya tashi Kowa yafara fada awajan.

Marigayi sani Garba Sk Shi yayita bin jaruman Yana Basu hakuri tareda cewar su kwantar da hankalinsu insha Allah Babu Wanda Zaici musu hakkinsu cikin ikon Allah Kuma sani Garba Sk yayi nasara wajan kwato musu hakkinsu.

Haka zalika Marigayi sani Garba Sk yashiga kungiyar hidima ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad s.a.w ma’ana kungiyace ta yabon manzon Allah, inda suke rera kasida Haka zalika Marigayi sani Garba Sk shima yayi kasidu dayawa acikin wannan kungiyar.

Abokan sana’ar sani Garba Sk sun shaidu jarumin cewar idan yazo wajan aiki baya Wasa da aikinsa Kuma idan yazo yana girmama kanana da jarumai Koda kuwa Yasan ya girmeka a shekaru.

Wannan kyawawan dabi’u da halayen Marigayi sani Garba Sk yasa mutuwarsa tayi matukar girgiza kannywood domin sunyi babban Rashi.
Muna rokon Allah ya jaddada Rahama agaresa Amin.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button