Wata sabuwa Sheik Ali Isah Pantami Mahaifinane Inji Adama Matar Kamaye

Fitacciyar jarumar kannywood zahra’u Saleh Pantami Wanda akafi sani da Adama Matar Kamaye acikin Shirin Dadinkowa Wanda yake zuwa agidan talbijin na tashar arewa24 duk Ranar Asabar da misalin karfe takwas na dare ta bayyana cewar sheik Isa pantami mahaifinta ne.

Jaruma Adama Matar Kamaye ta bayyana cewar an haifeta a garin Gombe Kuma tayi makarantar primary da secondary dukka acikin garin gombe.

Jarumar zahra’u ta bayyana cewar Dalilin Dayasa tace shaik Ali Isa pantami mahaifintane shine duk Wanda akaji Yana amfani da sunan (pantami) to Dan gidansu ne, Kuma Mal Sheik Ali Isa pantami kanin Mahaifinane Dan Haka kuwa yazama mahafina.

Adama ta bayyana cewar Dama tanada sha’awar Shiga harkar Fina finan Hausa, bayan tadawo daga saudiyya ita da kawarta hajiya zulai bebeji tafada Mata burinta nashiga harkar wasan Hausa.

Adama Matar Kamaye ta bayyana cewar tashiga harkar kannywood ta hanyar Musa Mai Sana’a inda shine mutum na farko daya Fara sakata acikin wani film nasa maisuna (Hisabi) daganan Kuma tafara samun Fina finai daban daban inda Marigayi Sani Garba Sk da Alhassan kwalle (Bakin wake) sune Suka zama jagororinta a masana’antar kannywood.

Haka zalika Adam takara da cewar tagodewa Allah akan yadda tasamu damar shiga cikin Shirin Dadinkowa domin lokacin dataje domin a tantance jaruman dazasu fitowa sunfisu 70 Amman cikin hukuncin ubangiji ita kadai tasamu wannan damar.

Adama tace babu Soyayya tsakaninta da Kamaye kamar yadda mutane suke daukar cewar tana Soyayya tsakaninta da Kamaye ta daukesa a matsayin uba Kuma Yaya Wanda duk lokacin data aikata wani Abu Wanda ba dai dai ba zaifito ya fada Mata domin tagyara.

Takara da cewar da zarar tasamu Miki zatayi aure domin haryanzu Bata samu mijin datakeso ba domin harkar aure abune dayake bukatar nutsuwa kwarai dagaske.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button