Wata sabuwa tsakanin Nafisat Abdullahi da Aisha Najamu izzar so akan maganar Aure

Jarumar Nafisat Abdullahi Wanda tana daya daga cikin jarumai Mata acikin masana’antar kannywood da ake ganin girmansu da mutuncinsu bisa irin kokari datayi wajan cigaban sana’arta Dakuma girmama nagaba da ita acikin masana’antar.

Fitacciyar jarumar kannywood nafisa Abdullahi tayi wani Jan hankali ga Mata budurwaye Yan uwanta akan yakamata suyi hankali sudinga gujewa wasu abubuwa tunkafin lokaci ya kure musu.

Nafisat Abdullahi ta bayyana cewar yakamata Yan Mata sudinga Gane samari mayaudara domin kuwa duk namijin dazaizo wajanki ya Bata shekara daya har zuwa shekara biyar toba mijin aure bane kirabu dashi ki nemi wani.

Domin duk namijin dazaizo wajanki da niyyar aure baya wuce kuyi dadewar shekara daya dashi sabida Shi baizo da Wasa ba Haka zalika bayazo bane domin ayita Soyayya kullum.

Saidai tun bayan wannan shawarar da jarumar ta bayar wasu daga cikin masoyanta sukaita Mayar Mata da martani inda suke fadin cewar maganar bahaka bane yakamata ta gyara kalamanta.

Domin akwai namijin da dagaske aurene acikin ran nasa Amman akwai abubuwan dayake shiryawa Wanda hakan zai iya daukarsa tsawon lokaci wani shekara daya wani shekara biyu ya danganta.

Bakowani Saurayi bane danyayi shekara uku kokuma hudu da mace bane za’a kirasa da mayaudari kokuma Wanda baishirya yin Aure ba cewar masoyan jarumar acikin raddin dasukai Mata.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button