Innalillahi Ashe Wannan shine Dalilin Dayasa aka cire Sumayya daga cikin Shirin labarina

Makallata Shirin labarina Mai dogon zango sun nuna Bakin cikinsu lokacin da rahoton ficewar jaruma sumayya ya bayyana a kafofin sada zumunta a daren ranar lahadi 02/01/2022.

Tabbas Shirin labarina zai iya fuskantar kalubalen makallata domin akwai mutanen dayawansu suna kallon Shirin ne Dalilin Soyayyar dasukema jarumar Nafisat Abdullahi wato sumayya.

Saidai jarumar Nafisat Abdullahi ta wallafa wata gajeruwar wasika a shafinta na Instagram zuwa ga Kamfanin Saira Movies nacewar daga yanzu tadaina fitowa daga cikin Shirin labarina sakamon wasu dalilai na kashin kanta.

Jarumar tayi godiya ga Kamfanin Saira Movies da irin gudunmawar dasuka bata wajan aikin Shirin labarina Haka zalika ta godewa masoyanta dasuke kokarin ganin cewar duk ranar juma’a sun tsaya domin kallon Shirin labarina a tashar arewa24.

Rahotanni sun bayyana cewar jarumar Sumayya yanzu batada ra’ayin fitowa acikin Fina finan Hausa domin a halin yanzu angano cewar jarumar tasaka kasuwancinta ne agabanta kadai kamar yadda sauran jarumai Mata na masana’antar kannywood sukeyi.

Kasancewar yadda kasuwar harkar Fina finan Hausa tadawo kan manhajar YouTube yasa manya manyan jarumai Mata na masana’antar Suka rungumi harkar kasuwanci domin tsira da mutuncinsu kasuwancin dasuka shafi Saida atamfofi, shaddodi, takalma, Gyale, riguna na maza Dana Mata dada sauransu.

Masoyan jaruma Nafisat Abdullahi sun matukar nuna Bakin cikinsu akan rashin cigaban fitowar jarumar tasu acikin Shirin labarina Mai dogon zango.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button