Innalillahi abinda yasa aka cire Nafisat Abdullahi aka canjata da Fati Washa acikin Shirin labarina

Shirin labarina ya kasance Shirin wasan Hausa Mai dogon zango Wanda akai kiyasin yafi kowani shiri samun makallata ayayin da ake nunasa a tashar arewa24 duk Ranar Juma’a da misalin karfe 9:00pm na dare.

Saidai tun bayan labarin rashin cigaba da ganin sumayya da Yan kallo bazasuyu ba acikin Shirin labarina series yasa makallata Shirin sukaita bayyana irin Bakin ciki tareda nuna halin damu akan cire Sumayya acikin Shirin.

Bayan Fitar da wata gajeruwar wasika a shafinta na Instagram jaruma Nafisat Abdullahi inda ta aika sakon izuwa Kamfanin Saira Movies tareda sanarda masoyanta Dake kallon Shirin labarina cewar bazata samu damar cigaba da fitowa acikin Shirin ba sakamakon wasu dalilai.

Cikin Dalilin jarumar ta bayyanar lokacin da Kamfanin Saira Movies sukabata domin tazo acigaba da aikin Shirin labarin ita Kuma a wannan lokacin akwai abubuwan dazatayi ta bukaci Kamfanin Daya daga lokacin daukar Shirin izuwa nangaba inda Kamfanin ya nuna Bai amince da wannan bukatar tata ba.

Da hakane jarumar ta bayyana cewar itama bazata iya dakatar da Abubuwan dazatayi ba domin zuwa cigaba da daukar Shirin labarina wannan Dalilin yasa Kamfanin Suka yanke hukuncin sauyata dawata jarumar domin gujewa kurewar lokaci.

A gefe guda Kuma darakta Shirin labarina Mal Aminu Saira a kwanakin baya ya taba wallafa wani hoton jaruma Fati Washa a shafinsa na Instagram inda yayi gajeran Rubutu a kasan hoton yake cewa (idan Fati Washa) ta bayyana acikin Shirin labarina wani gurbi kuke ganin Zata cike?) Wannan tambayar yayita ne izuwa ga Yan kallo.

Inda mutane sukaita bayyana ra’ayinsu a kasan hoton wasu suna fadin cewar Fati Washa yakamata ta maye gurbin Laila acikin Shirin labarina inda wasu suke fadin yakamata ta maye gurbin sumayya acikin Shirin labarina.

koma dai menene kukasance da shafin Arewajoint domin Samun cigaban wannan labari tareda wasu labaran kannywood Dama labaran Duniya Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button