Kanwar Nafisat Abdullahi maisuna Radiya Zata maye gurbin ta acikin Shirin labarina

Kamar yadda Shirin labarina yacire tuta akan sauran Fina finan Hausa masu dogon zango wajan kayatarwa fadakarwa gami da nishadantarwa duk a lokaci daya.

Barin Nafisat Abdullahi wato sumayya daga cikin Shirin tabbas ka iya sawa wasu daga cikin makallata Shirin sudaina kallonsa kamar yadda sukaita fada a ranar da jarumar ta bayyana cewar baza’a Kara ganin fuskarta ba acikin Shirin labarina.

Sakamakon lokacin da Kamfanin Saira Movies sukeso suci gaba da daukar cigaban Shirin yayi dai dai da lokacin da jarumar take wasu harkokin kasuwancinta inda aka Kasa samu dai daito tsakanin jarumar da Kamfanin Saira Movies wannan Dalilin yasa jarumar ta bayyana cewar ita ta hakura da fitowa acikin Shirin.

Saidai tun bayan bayyana cewar tadaina fitowa acikin Shirin wani bidiyon kanwar Nafisat Abdullahi maisuna Radiya yanata yawo a kafofin sada zumunta inda mutane suke bayyana cewar itace Zata maye gurbin Yar uwartata acikin Shirin labarina.

Radiya takasance kanwar Nafisat Abdullahi tajini ce Kuma suna matukar Kama sosai wannan Dalilin yasa mutane sukaita bayyana ra’ayinsu na cewar a maye gurbin Nafisat Abdullahi da kanwartata kawai. Gadai wani cikakken videon kanwar Nafisat Abdullahi domin kugani.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button