Ganin sabon hoton Maryam Yahaya a wannan yanayin yasa mutane sunshiga wani Hali

Tun bayan samun lafiyar jaruma Maryam yahaya a karon farko jarumar ta halarci wani bikin yaron producer Abdulamart maikwashewa Wanda aka Gudanar dashi acikin garin Kano.

Inda awajan Shagalin bikin anga jarumar tareda kawayenta dawasu sauran jarumai nacikin masana’antar kannywood kasancewar bikin ya hada manya manyan jarumai dasuka halarci wajan taron.

Saidai tun bayan bayyanar hotunan jarumar akaga yadda alamu Suka nuna cewar Haryanzu jarumar Bata Gama warkewa ba domin fuskarta da hannunta sun nuna alamun rama a tattare da ita.

Wannan Dalilin yasa wasu masoyan jarumar Suka fito suka nuna rashin jindadinsu tareda Bata shawarar cewar yakamata tadaina daukan hotunanta harzuwa lokacin da Allah zaibata lafiya tadawo dai dai.

A kwanakin baya sadiya haruna Mai Saida maganin Mata itama tafito tabawa Maryam yahaya shawara Kan cewar yakamata tayi hakuri tasamu lafiya saita dinga hotuna tareda videos domin yadda take fitowa tana hotuna hakan Yana Kara Bawa makiyanta damar dazasu sake cutar da ita.

Haka zalika jarumar kannywood hajara Aliyu itama a kwanakin baya tafito tabawa Maryam Yahaya shawarar tadaina hotuna da video, saidai daga baya Kuma hajarar taciro bidiyon datayi akan jarumar a shafinta na Instagram Wanda bamusan Dalilin hakan ba.

Saidai har izuwa yanzu jaruma Maryam yahaya Bata taba fitowa tayi martani akan mutanen dasuke fitowa domin subata shawara kokuma ta nuna bacin ranta ko akasin hakan ba.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button