Adam a zango ya tallafawa Marayu da kudi Naira miliyan biyu N2,000,000

Fitaccen jarumin acikin masana’antar kannywood Adamu Abdullahi zango ya tallafawa Marayu da marasa karfi Wanda suka koyi sana’ar hannu karkashin gidauniyarsa da kudi kimanin naira miliyan biyu.

Cikin wani yunkuri na ganin antaimakawa marasa karfi Dakuma Marayu domin Samun sana’ar dazasu dogara dakansu gidauniyar Jarumi Adam a zango ta Shirya taron koyarda Sana’a kyauta harna tsawon kwanaki uku a garin Kaduna.

Cikin ikon ubangiji bayan kammala wannan taron koyarda sana’ar hannu kyauta ranar da aka Shirya domin yaye daliban dasuka koyi wannan sana’ar Jarumi Adam a zango ya halarci wajan wannan taron inda yabada kyautar kudi har naira miliyan biyu N2,000,000 domin a tallafawa Wanda suka koyi sana’ar da jari.

Idan Mai karatu bai mantaba a shekarun baya Jarumi Adam a zango ya taba daukar nauyin biyawa Marayu kudin makaranta a garin Zaria, lokacin Marigayi sarkin zazzau Shehu Idris da kimanin kudi naira miliyan arba’in da wani abu.

Ga video

Ku Danna alamar kararrawar dakuke gani agabanku domin kasancewa da shafinmu maisuna Arewajoint akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button