Video Shagalin biking Rahama Sadau da Yakubu Muhammad Ya Girgiza Kannywood

Wasu kyawawan hotunan Fitattun Jaruman Kannywood guda biyu kenan Wanda suka shahara a masana’antar kannywood Dakuma Nollywood Dake kudancin najeriya.

A jiya dai hotunan Rahama Sadau da Yakubu Muhammad saukaita yawo a kafofin sada zumunta inda ake bayyana cewar jaruman guda biyu zasuyi aurene domin yanayin hoton yayi alamu da irin Wanda ma’aurata sukeyi lokacin aurensu.

Saidai munyi kokari wajan gano cikakken gaskiyar wannan lamarin inda da farko dai hoton Rahama Sadau da Yakubu Muhammad ba hoton aure bane, hoto ne Wanda aka dauka na sabon Shirin Kamfanin Rahama Sadau maisuna (Sadau pictures).

Matar aure dai shine zai zama sabon Shirin jaruma Rahama Sadau a shekarar 2022, tun bayan dakatar da ita da masana’antar kannywood tayi.

Saidai bayyanar wannan hotunan ya nuna jaruma Rahama Sadau tadawo masana’antar kannywood tun bayan dakatar da ita da akayi a shekarar 2021 lokacin tana nuna wani shirinta maisuna “Yar Minista” a shafinta na YouTube.

TUNA BAYA

Idan baku mantaba dai an Dakar da jaruma Rahama Sadau a shekarar data gabata wato 2021 sakamakon wata shiga datayi ya fidda tsaraicinta inda wani yayi batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad a kasan hoton jarumar a shafinta na Twitter.

Wannan Dalilin yasa masana’antar kannywood tadauki babban hukunci wajan dakatar da jarumar domin hakan yazama izna ga sauran jaruman dasukeda niyyar aikata abinda jarumar ta aikata.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button