Yadda aka Gudanar da Shagalin bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Zainab indomea

Tsohuwar jarumar kannywood Zainab indomea tayi bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta a jiya Asabar 15/01/2022.

Hotuna tsohuwar jarumar kannywood Zainab indomea sun karade kafofin sada zumunta na social media inda akaita wallafa hotunan jarumar tareda yimata addu’ar Allah ubangiji yakaro Mata shekaru masu albarka da Karin lafiya.

Saidai a gefe guda masoyan Zainab indomea yazama kamar an Sosa musu inda yake musu kaikaiyine domin ajiya sunyita tambayar shin Ina jarumar tasu tashiga ne ganin yanzu andaina ganinta acikin sababbin Fina finan Hausa.

Zainab indomea dai shekaru biyu zuwa uku tasake dawowa harkar film inda akaga wasu hotunanta a shafin fitaccen jarumin kannywood Adam a zango Yana nuni da cewar jarumar tadawo masana’antar kannywood Kuma tadawo da zafinta.

Saidai Jim Kadan bayan wasu lokata da aka dauka ba’a sake jin jarumin yayi magana akan jarumar ba Haka zalika ba’a sake ganin ya wallafa hoton jarumar akan shafinsa na Instagram dinba.

Saidai har izuwa yanzu rahotanni sun bayyana cewar Zainab indomea batayi aure ba Haka zalika, bata cikin masana’antar kannywood zamu iya cewar idan jarumar tana bibiyan shafin Arewajoint yakamata ace tana fitowa kafofin sada zumunta domin masoyanta suna matukar marmarin son ganinta.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button