Nafisat Abdullahi Ta Bayyana Irin Halinda Tashiga Bayan Barin Labarina

Makonni biyu dasuka wuce dai wani abun alajabi ya faru inda fitacciyar jarumar kannywood Nafisat Abdullahi tafito tabada sanarwar cewar baza’a sake ganin fuskarta acikin Shirin labarina ba.

Bayan wallafa wannan sanarwar a shafinta na Instagram masoyan jarumar sun nuna rashin jindadinsu inda a wannan lokacin sukaita tura Mata da sakonni iri daban daban akan cewar meyasa zata fita daga cikin Shirin labarina a lokacin da ake bukatarta.

Nafisat Abdullahi ta bawa wasu daga cikin masoyanta amsa bayan tamboyoyin dasuka tura Mata kamar Haka:
Bawai nabar Shirin labarina sabida munyi fada kokuma wani abu na dabanbane, nabar Shirin ne sabida lokacin da Kamfanin suke bukatar aiki dani a lokacin nikuma inada nawa ayyukan daya kamata nayi a wannan lokacin. Kamfanin sunga bazasu iya jirana ba Kuma nima bazan iya janye ayyukana ba wannan Dalilin yasa Banida wani zabi face na hakura da cigaba da fitowa acikin Shirin labarina.

Duk da amsar da Nafisat Abdullahi ta bawa masoyan nata hakan bai hana wasu masoyan nata dacigaba da bata hakuri akan tadawo domin sun matukar Ƙaunar ganinta acikin Shirin na labarina. Saidai jarumar tabawa masoyan nata hakuri tareda cewar zasu ganta acikin wani sabon Shirin nan bada jimawa ba.

Saidai bayyanar wasu sababbin bidiyo da hotunan Nafisat Abdullahi sun bayyana irin sabuwar rayuwar da jarumar tashiga tun bayan barinta Shirin labarina kamar yadda zaku gani acikin wannan bidiyon.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button