Kalli video Gaskiyar Maganar Dawowar Sumayya acikin Shirin labarina season 5

Tabbas Fitar Nafisat Abdullahi daga cikin Shirin labarina zai ragewa Shirin tagomashi awajan wasu makallata Shirin sakamakon akwai Wanda suka bayyana cewar sanadiyyar Nafisat Abdullahi suke kallon Shirin labarina.

Tabbas labarin shirine wanda ya tara manyan jaruman kannywood Kuma ya kasance shine Shirin dayafi samun Miliyoyin makallata a duk lokacin da ake nunasa a tashar arewa24 a duk ranakun juma’a.

Saidai ayanzu ba’asan a wace matsaya aka tsayaba tun bayana sanarwar da jaruma Nafisat Abdullahi ta Fitar nacewar masoyanta sudaina Zaman jiran sake ganin fuskarta acikin Shirin labarina, domin kuwa bazasu Kara ganin fuskarta ba acikin Shirin.

Nafisat Abdullahi ta bayyana cewar baza’aci gaba da nuna fuskarta acikin Shirin ba amman masoyanta suyi hakuri domin Nan bada jimawa ba zasu ganta acikin wani sabon shirinta.

A gefe guda Kuma jiya wasu rahotanni tareda hotunan Nafisat Abdullahi ne akaita wallafa a kafofin sada zumunta na Facebook inda ake bayyana cewar jarumar tace Zata dawo cikin Shirin na labarina, saidai munyi kokari wajan tabbatar da wannan labarin.

Labarin ba gaskiya bane domin kuwa Nafisat Abdullahi a shafinta na Instagram Bata Fitar da sanarwar cewar Zata dawo Shirin labarina ba, Haka zalika mahukunta Shirin labarin Basu bayyana cewar Jaruma Nafisat Abdullahi Zata dawo Shirin ba a halin yanzu saidai bamusan ko anan gaba ba.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki da akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button