Innalillahi Manyan Jaruman Kannywood Sunshiga Tashin hankalin akan Kisan Hanifa da akayi

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un manyan jaruman kannywood sun matukar shiga Tashin hankali Kan irin yadda malamin makarantarsu Hanifa ya kasheta agidansa sannan ya dauki gawar ya binne acikin harabar makarantarsa.

A jiya jaruman kannywood manyansu da kananan sunshiga sahun masu alhinin abinda ya faru da karamar yarinya Hanifa Yar shekara biyar da haihuwa Wanda ta Bata tun acikin watan dizembar shekarar 2021.

Inda akaita bada sanarwar a wancan lokacin gidajen radiyo da police station, inda aka bayyana cewar haifar dai ana zargin an dauketane acikin adaidaita sahu wato (Keke napep) bayan dawowarta daga islamiyya.

Inda cikin hukuncin ubangiji Bayan Bincike da hukumar DSS da Yan sandan najeriya reshen Jahar Kano Suka gudanar ankama shugaban hukumar makarantarsu Hanifa aka tuhumesa tareda amsa cewar shine ya Kashe Hanifa Kuma ya binneta acikin harabar makarantarsa.

Inda aka sakashi agaba shida abokinsa daya taimaka Masa wajan binne wannan yarinyar izuwa makarantar inda aka tono gawar Hanifa acikin wani buhu.

Jaruman Kannywood irinsu Ali Nuhu, Hassan giggs, Hadiza Gabon, Amal Umar, Aysher Humairah, Abubakar Bashir maishadda, Adam a zango, Aminu Saira, sunusi Oscar, Yakubu Muhammad.

Suna daga cikin jaruman dasuka jajantawa iyayen Hanifa akan wannan abu daya faru dasu tareda rokon gwamnati ta yankewa Wanda ya aikata wannan abun hukunci dai dai da abinda ya aikata.

Haka zalika a gefe guda Kuma zakuji cikakkiyar sautin muryar mahaifin Hanifa a lokacin da BBC Hausa sukai Hira dashi a wannan bidiyon na Kasa.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button