Mahaifiyar Hanifa ta Fashe da Kuka ganin yadda akayi gunduwa gunduwa da gawar Hanifa innalillahi

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un tabbas wannan alamari daya faru da karamar yarinya Yar shekara biyar ya matukar dagawa mutanen Duniya hankali Harda Wanda bama musulmai ba.

Cikin wata Hira da gidan jaridar BBC Hausa sukayi da mahaifin Hanifa ya bayyana irin kuncin Rayuwar dasuka Shiga na tsawon kwanaki arba’in da wani abu tun lokacin bacewar yarinyar tasu.

Haka zalika mahaifin Hanifa ya bayyana cewar tun lokacin batar Hanifa mahaifiyarta dashi suka shiga Tashin hankalin dayayi sanadiyyar kwantar da mahaifiyar Hanifa a kwance a Gadon asibiti.

Mahaifiyar Hanifa ta bayyana cewar Bayan samun gawar Hanifa da akayi ba’a kawota gida ba ballema tagani da idanunta domin yadda aka fadamata yadda aka sami gawar acikin buhu ya matukar tada hankalin ta innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, gadai cikakken bidiyon Hira da mahaifin Hanifa.

Ga video

Allah ubangiji yaji Kan Hanifa da Rahama yasa Aljanna makomarta.
Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button