Cikakken videon Yadda wasu Matasa Suka Kona Makarantarsu Hanifa karfe dayan dare

DA DUMI-DUM: wasu fusatattun Matasa sun kone daya daga cikin makarantar malamin su Hanifa Wanda yayi garkuwa da ita daga baya Kuma ya kasheta.

Wasu fusatatattun matasa sun bankawa ginin makarantar Noble Kids da ke kan titin Warshu Hospital, Kawaji Kano wuta saboda kashe daliba yar shekara Biyar mai suna Hanifa Abubakar da mai makarantar yayi bayan yayi garkuwa da ita.

Rahotanni sun bayyana cewar da misalin karfe 1:30pm na dare wasu Matasa Wanda ba’asan ko suwaye ba sun dira makarantasu Hanifa inda suka Cinna Mata wuta Nan take tafara kone.

Saidai wasu mazauna unguwan sun shaida cewar lamarin yasa Ankira motar (fire service) kasancewar wutar takusa shafan gidajen dake kusa da ginin makarantar dakeci da wutar, ,inda hada da taimakon Yan unguwar aka samu aka Kashe wutar.

Ga cikakken videon

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button