Wata babbar Kotu a Kano tabada umarnin akamo jarumin kannywood Sadiq Sani Sadiq akan laifin daya aikata

Wani labari damuke samu da dumi duminsa wata babbar Kotun musulunci Dake zamanta a hotoro masallaci garin Kano karkashin Mai Shari’a Sagir Adamu tasa akamo fitaccen jarumin kannywood Sadiq Sani Sadiq sakamon bijirewa umarnin Kotun.

Tunda fari dai wani producer Mai Shirya fina finan Hausa maisuna Aliyu Adamu Anas yayi karar jarumin sakamon bawa Sadiq Sani Sadiq wani Abu daga cikin kudin aikin dazaiyi Masa Kuma jarumin baizo yayi Masa aikin ba, Kuma bai mayarwa da Mai Shirya Fina finan kudinsa ba, wannan yasa Aliyu Adamu Anas yakai Kara gaban kotu domin tabi Masa hakkinsa.

Idan baku mantaba a kwanakin Bayama wani Kamfanin UK Entertainment sunkai karar Daya daga cikin jaruman kannywood wato hafsat Idris Kan karban kudinsu domin gudanar wani aiki inda akarshe batayi aikin ba, saidaga baya sarki Ali Nuhu yashiga maganar domin sasantawa.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button