Allah sarki yan film zasuyi sabon Shiri akan kisan Hanifa da malamin makarantarta yayi Mata

Idan baku mantaba dai a Makon daya wucene dai hukumar Yan sandan Jahar Kano Suka Kama Abdulmalik Tanko malamin Hanifa Wanda yayi garkuwa da ita acikin gidansa.

Bayan kamashi tareda amsa laifinsa da rakiyar hukumar Yan sandan Jahar Kano anje daya daga cikin makarantun Abdulmalik Tanko inda aka tono gawar Hanifa da binne awajan.

Alumma sunyi matukar jimami Kan irin wannan musifar data faru da karamar yarinya Yar shekara biyar da haihuwa, inda mutane da dama sunyita tofa albarkacin bakinsu a kafofin sada zumunta Kan wannan alamarin daya faru.

Saidai wani labari daya fito daga shafin BBC Hausa a dandalin Facebook sun bayyana cewar wasu daga cikin masana’antar kannywood sun Shirya film din hausa maisuna (Hanifa) saidai mutane da dama sunyita bayyana ra’ayinsu inda wasu suke ganin hakan yadace wasu Kuma suke ganin hakan baidace ba.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button