Abun boye yafito fili mawaki Lillin baba zai Auri Ummi Rahab Masha Allah

Daya daga cikin mawakan kannywood Kuma Jarumi acikin Shirin “WUFF” lillin baba ya bayyana cewar insha Allah yakusa yayi WUFF da abin kaunarsa wato Ummi Rahab.

A lokacin da mawakin yake Taya Ummi Rahab murnar zagayowar ranar haihuwarta, inda ya wallafa wasu kalamai masu ratsa zuciya a kasan hotonta daya daura a shafinsa na Instagram tareda yimata addu’ar Allah yakawo shekaru masu albarka.

Soyayya Mai karfi tafara kulluwa tsakanin Ummi Rahab da lillin baba tun lokacin rabuwar Ummi da Adam a zango sanadiyyar wata matsala dasuka samu wanda har hakan Yayi sanadiyyar da Adam a zango yacire Ummi Rahab din daga shirin maisuna “Farin wata”

Duk wani makallacin Shirya Fina finan Hausa shekara goma baya dasuka wuce Yasan wacece Ummi Rahab kasancewar tun tana karama take fitowa acikin Fina finai daban daban, Kuma duk wanda yasanta a lokacin baya yasantane tareda Jarumi Adam a zango.

Akwai ma Wanda suke tunanin cewar Adam a zango shine mahaifinta kasancewar yadda Ummi Rahab take Kiran Adam a zango da (Daddy) ma’ana banana.

Wasu daga cikin jarumai a masana’antar kannywood sunyiwa lillin baba da Ummi Rahab addu’ar Allah ubangiji yakawo lokacin dazasuga auren lillin baba da Ummi Rahab.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin Samun labarai cikin sauki akoda yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button